Tuesday 23 April 2024

Karanta Labarin Gaggawa Da Hakuri Da Lokaci

Karanta Labarin Gaggawa Da Hakuri Da Lokaci

Watarana, wasu matasa biyu Gaggawa da Hakuri suna tafe a cikin wani ƙungurmin daji mai suna Duniya, a ƙoƙarin su na neman wani lambu mai suna Nasara. Tare da su akwai wani yaro ɗan ƙarami, mai suna Lokaci, wanda yake yi musu rakiya.


LABARIN GAGGAWA DA HAKURI DA LOKACI
Hoto: PNGTREE


 

Marubuci: Muhammad Musa Yelwa


Su na tafe suka isa wani kwazazzabo mai yawan duwatsu, wanda kuma a wurin ne ɗan rakiyar tasu Lokaci ya yi tuntuɓe da dutse, ya faɗi! Kodayake, ya lallaɓa ya yi ƙarfin hali ya tashi, sai dai yanzu tafiyar tasa babu sauri, sakamakon jan-ƙafa da yake yi.


Su na cikin wannan hali ne kuma Gaggawa ya hango wancan lambu da suke ta faman nema. Don haka, nan take ya ruga a guje, ya nufi wurin.


Lokaci ya ƙwalla masa kira:

“Haba Gaggawa, ya za ka yi mana haka? Ka jira mu mu shiga tare mana.”


Gaggawa ya ci gaba da gudunsa, ba tare da ya ko waiwaya ba. Ganin haka, Haƙuri ma ya ƙara ɗaga murya, yana cewa: “Kai kuwa wanne irin ci-da-zuci kake haka? Ka tsaya mu mana.”.


Gaggawa ya juyo a fusace ya ce da shi: “Kai rufe min baki, ni ba ni da kai.”.


Lokaci ya juya ya dubi Haƙuri ya ce: “Ka ji fa, wai ba shi da kai. Yana nufin ya haukace ne?”.


Haƙuri ya ce: “A’a, yana nufin dai ba shi da kai ne, wataƙil.”


Lokaci ya gyaɗa kai, sannan ya ce: “To kai me ya hana ka ka bi shi?”


Haƙuri ya ce: “Ni ba na tashi ai.”


Lokaci ya ce: “Kana nufin ba ka da fuffuke kenan?’’


Ya ce: “Ina nufin ba na gaggawa.”


Lokaci ya ce: “To me ya sa?”


Ya ce: “Saboda ina sane da cewa, ko da na je zan taar da ƙofar lambun a rufe. Tun da dai babu wani abu da yake faruwa ba tare da lokaci ba. kuma ga ka a nan.” 


Lokaci ya yi murmushi, sannan ya ce: “Hakika ka yi kyan kai. Tabbas mabuɗin yana tare da ni, amma tun da ka yi haƙuri, karɓi mukullin daga yau na ba ka kyauta, ya zama naka.” 


Suna ƙarasawa bakin lambun kuwa, Haƙuri ya sa mabuɗi ya buɗe lambun Nasara, ya yi bankwana da lokaci ya shiga. Yana tunanin shin ko a ina Gaggawa ya maƙale!?”


Yayin da Lokaci ya juya don ci gaba da tafiya, sai ya hangi Gaggawa kwance magashiyyan a bayansa, yana numfarfashi, ashe zuwa ya yi ya riƙa bangazar ƙofar ba ta buɗe ba har sai da jikinsa ya yi la’asar (Sanyi). Can cikin wata murya mai raurawa, ya ce wa Lokaci: “Don Allah ko akwai wani mabuɗin ka taimaka ka ba ni, ni ma na shiga?”


Lokaci kuwa ya ce da shi: “Ai mabuɗin Nasara ɗaya ne, kuma tuni yana tare da Haƙuri. Da ka yi haƙurin jira na, da ka samu, amma da yake ba ka yi ba, ga shi nan har na riga na wuce. Kuma ni idan na wuce ba na dawowa baya.” .


Don ci gaba da samun ire-iren waɗannan, ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.

Sunday 21 April 2024

Karanta Zafafan Sakonnin Barka Da Sallah Na Zamani Masu Ratsa Sassan Jiki Da Zuciya

Karanta Zafafan Sakonnin Barka Da Sallah Na Zamani Masu Ratsa Sassan Jiki Da Zuciya

KYAWAWA


Na ga kyawawa amma ban ga tamkar ki ba. Na ga lalle amma ban ga irin naki ba. Sun saka kaya, amma ba su yi musu kyau irin naki ba, ba wai zuzuta ki nake ba, idan na ce da a ce kin bai wa maza fuska a yau, da kuwa na rasa ki. Hmm kyawu sai mai shi. Ado sai gidansa. Barka Da Sallah 'Yammata. Ina son ki!


Saƙonnin Barka Da Sallah
Hoto: Freepik


BURGE


Abin da zan faɗa miki a yau, abu ne wanda da a ce madubi yana magana, zai faɗa miki kafin ni, kin haɗu, ma'ana kin yi matuƙar haɗuwa, duk namijin da kika wuce ta gabansa, koda bai faɗa ba a zahiri kin ji ba, na tabbata dole a zuciyarsa sai ya ce MASHA ALLAH!. Ba maganar mata ake ba, don ko ba a faɗa ba, dole za su yi miki hassadar kyawun da kika yi. An matuƙar burge ni. Barka Da Sallah. Ina son ki!


SAFIYA 


Kyakkyawar safiyar rana ta musamman zuwa ga wacce murmushin ta kaɗai haske ne, da ka iya kore duhun zuciyar namiji ko shi wane ne, ko ba lalle sabon ɗinki ko kwalliya, ɗari bisa ɗari na yi imani sai kin fi kowa haskawa a yau, ba na shakka na saka ko nawa ne kan cewa sai kin fi kowacce mace ɗaukar ido da samun makalla (Masu kallo/Masu Gani). Na yarda da gwanata. Barka da sallah. Ina son ki.


HOTO


Kwanaki talatin, sa'o'i ɗari bakwai da ashirin, mintina dubu arba'in da uku da ɗari biyu, daƙiƙu miliyan biyu da ɗari biyar da dubu casa'in da biyu, na shafe ina kintata yadda kwalliyar ki ta yau za ta kasance, na bijiro da hotunan ki cikin kwalliya daban-daban, amma har zuwa yau ƙwaƙwalwata ta kasa tsai da hoto ɗaya wanda ya dace da irin kyawun da za ki yi a yau. Ina fatan ko ban zamo na farko ba, kada na zamo na ƙarshen da zai ga irin kyawun da kika yi a yau.


KWALLIYA


Kin fasa zuciyata da kwalliyar ki 'Yammata, kin ƙafar da ruwan idanuwana gurin kallon ki, kin hana bakina rufewa da haɗewar ki, kalma ɗaya tak ta rage a kalaman bakina shi ne an burge ni. Kyawun da kika yi a yau 'Yammata ya wuce na ce komai face Allah ya kare min ke daga masu kambun ido. Barka da sallah.


ƊARI


Idan za ki rayu na tsawon shekaru ɗari a duniya, ni kuma zan so na rayu na tsawon shekaru ɗari ba ɗaya, domin ba zan so na rayu a cikin wunin da babu ke a cikin shi ba. Idan ma'anar soyayya shi ne fifita farin cikin wanda kake so fiye da naka farin cikin. To, kuwa har abada 'Yammata farin cikin ki ne a saman nawa farin cikin. Sannan saka ki farin ciki nauyi ne a gare ni, wanda matuƙar ban sauke wannan nauyin ba, har abada ba zan taɓa samun natsuwa a zuciyata ba. Ina son ki.


SOYAYYA


Idan na faɗi a ko'ina ne zan tashi na ci gaba da tafiya, amma daga lokacin da na faɗi a soyayyar ki wataƙil ba zan kuma tashi na tsawon rayuwata, faɗuwa a jarabawa ko a neman aiki da kasuwanci ba sa tayar min da hankali. Babban taraddadin zuciyata shi ne zamo wa mara nasara a soyayyar ki, fatana a kodayaushe na yi nasara a zuciyar ki, burina a kullum na mallake ki a matsayin mata a gare ni. Idan wannan burin nawa ya cika, har abada ba na da wata sauran damuwa. Ina son ki 'Yammata.


FUSKA


Zama a kusa da ke ko babu aikin komai shi ne kusan komai a gare ni, aikin kallon kyakkyawar fuskar ki kaɗai ya fiye min duk wani aiki da zan yi, domin kuwa 'yammata bambancin aikin kallon ki da sauran ayyuka shi ne sauran ayyuka gajiyar da ni za su yi. Aikin kallon ki kuma kore min gajiyar zai yi, don haka nake ganin shafe tsawon rayuwata ina aikin kallon ki ba zai taɓa gajiyar da ni ko ya sa min damuwa ba. Ina son ki.


TARIHI


A gurina duk ranaku ɗaya ne, idan ban da ranar da na fara ɗora idanuwana akan kyakkyawar ki, wannan ranar kam daban ce, tana da rubutaccen tarihi a zuciyata, tana da keɓantaccen muhimmanci a rayuwata, kuma tana da haske na musamman a raina, 'Yammata samun ki babbar ni'ima ce a gare ni, domin kuwa da shigowar ki rayuwata kika sauya komai a tare ni, kika ba ni farin ciki a madadin damuwa, kika ba ni haske a madadin duhu. Ina son ki.


TAMBAYA


Ke ce ranar da ke haska wunina, iskar da ke kaɗawa a sararin duniyata, numfashin da yake rayar da gangar jikina, haka ma wacce sunan ta ne rubuce a tarihin rayuwata, 'Yammata idan za ki tambaye ni ina son ki kuwa? Amsa ta a kullum za ta kasance sosai ma kuwa. Idan za ki tambaye ni zan iya barin ki a rayuwata? Amsa ta ga wannan tambayar shi ne koda wasa. Idan kuwa tambayar ki ta kasance wacce mace ce na fi so a rayuwata? Ko ƙarisa tambayar ba za ki yi ba, zan tare ki da amsar cewa ke ce.


FUSHI


Duk tsananin hasken da rana take da shi, hasken ta bai taɓa haskawa cikin zuciyata ba, amma shigowar ki rayuwata, sai ga shi hasken ki ya haske zuciyata fiye da yadda rana ke haska duniya, da haska zuciyata da kika yi, a yau kin zamo nuril ƙalbi (Hasken zuciya) kuma nuril hayati (Hasken rayuwa), 'Yammata zuwan ki cikin rayuwata ya kore dukkan duhun da na kasance a ciki, ke alkhairi ce a gare ni 'Yammata, ba zan taɓa rabuwa da ke ba, ba zan taɓa iya fushi da ke ba. Ina son ki.


KYAUTA 


Ni kawai roƙar Allah na yi ya ba ni azurfa, gwanin kyautar kuma sai ya ba ni zinare, ban taɓa sa ma kaina dogon burin samun kyakkyawar mace tamkar ki ba a rayuwata, amma sai ga Ubangiji ya ba ni ke 'Yammata, macen da ta fi kuma ta zarce sauran mata, wacce a matsayi sai dai a kira ta da gimbiyar mata, a ƙananun shekaru autar mata, a ilimi da sanin ya kamata kuma dole a kira ta da sayyadar mata, a zubi tsari da kyawun surar ki dole a kira ki sarauniyar mata ko maƙiyin ki ne ya ce ba ya son ki, bakinsa ne yake faɗar abin da ba shi ba ne a zuciyarsa ba. Ina son ki. 


DUNIYA


Zan saka ki farin ciki yayin da kika shiga damuwa, zan saka ki dariya yayin da wani ya ɓata ran ki, zan zamo bango yayin da kike buƙatar dafawa, zan zamo ƙwarin gwiwar ki yayin da kike da wani buri da kike son cimma wa, 'Yammata ko na faɗa ko kar na faɗa abu ne da kowa zai iya fahimta a tare da ni cewa na kamu da matuƙar son ki. Idan na kira ki da jannati, wannan don zamowar ki Aljannar Duniyata ce. Idan na kira ki da hayati, wannan don kin kasance rayuwata ce. Ina matuƙar son ki Jannati. Ina son ki!


Sanusi Kabir ne ya gabatar da su, wakilin mu ya fitar da su a rubuce, ga dukkan wanda yake son ya saurare su a ainihin yadda suke, zai iya sauke Audio ɗin ta hanyar latsa nan.

Hikimomin Rayuwa 5 Ga Masu Son Cimma Nasara

Hikimomin Rayuwa 5 Ga Masu Son Cimma Nasara

1. SAURARON GAZAWARMU – KARƁAR TSOKACI: Wato mafi yawancin muna da matsala wajen sauraron matsalolin mu, ko a ci gyaran mu. Hikimar sauraron tsokaci na ɗaukar lokaci wajen koyo da ƙwarewa, kuma yadda ake yi shi ne, ka kau da duk wani abu da kake ji a cikin zuciyarka, ka mayar da hankali akan bayanan da ake ba ka. Wani gyaran yana da amfani, wani kuma ba shi da shi. Ka yi amfani da ƙwaƙwalwarka wajen tantancewa, ba zuciyarka ba.


Hikimomin Rayuwa
Hoto: Unsplash


MarubuciBello Galadanchi


2. MIƘEWA BAYAN FAƊUWA: Kar ka karaya. Ka miƙe, ka watsake, sannan ka yi amfani da darrusan da ka koya domin ƙara wa kanka ƙarfin zuciya da taurin rai domin shiryawa gaba. Wannan hikima tana da wahala, amma sinadari ne mai muhimmanci idan har kana so ka samu ci-gaba a rayuwa.


3. BADA HAKURI: Dole sai ya fito daga zuci, kuma ka bayyana yadda za ka yi ƙoƙarin kiyayewa gaba. Kar ka bada haƙuri kamar haka:


"Ka yi hakuri saboda na ɓata maka rai. Hanzari nake shiyasa na yi wannan kuskure."


Ka gani anan, haƙurin ya mayar da hankali ne akan yadda wanda aka ɓatawa rai yake ji, ba abin da ka yi ba da yadda za ka kiyaye. A guji bada irin wannan hakuri.


Ga misali mai kyau:


"Ka yi hakuri saboda laifin da na yi. Na makara ne wajen tashi daga bacci shiyasa ban iso da wuri ba. Nan gaba, zan kwanta da wuri, sannan zan yi amfani da wayata wajen tuna min da lokacin da ya kamata na tashi."


4. GODIYA: Ka tantance mutanen da ke ba ka goyon baya da faranta maka rai, sannan ka bayyana musu yadda kake ji. Ka tabbatar sun san cewa suna da matuƙar muhimmanci a rayuwarka, kuma kana matuƙar darajanta su. Babu wanda zai iya rayuwa shi kaɗai a duniyar nan, saboda haka ka zama mai mutunci da zumunci.


5. FAHIMTAR ABUBUWAN DA SUKA FI MUHIMMANCI: Ka tabbatar ka yi amfani da lokacinka da kadarorinka akan batutuwan da suka fi muhimmanci. 


Mutane da yawa na cakuɗa abubuwa da yawa a rayuwarsu ta yau da kullum saboda ba su san ko mene ne ya fi muhimmanci ba.


Ka rubuta duk abubuwan da kake aiki akai, sannan ka jera su daga wanda ya fi muhimmanci a farko, zuwa wanda ba shi da tasiri sosai a ƙarshe. Ka rubuta lokutan da za ka aiwatar da su, sannan ka fara aiki. 


Allah Ya shige mana gaba.

Ku Hanzarta Sauke Zafafan Sakonnin Barka Da Sallah Na Zamani Audio Na Sanusi Kabir

Ku Hanzarta Sauke Zafafan Sakonnin Barka Da Sallah Na Zamani Audio Na Sanusi Kabir

Wannan Audio na "Barka Da Sallah Na Zamani" cike yake da zafafan saƙonnin soyayya masu ratsa sassan zukatan masoya, waɗanda su fi dacewa da masoyan zamani.


Saƙonnin Barka Da Sallah
Hoto: Dreams Time


Sanusi Kabir wanda aka fi sani da Limamin Masoya, ba ɓoyayye ba ne  a fagen nishaɗantar da masoya.


Idan har kana soyayya, lallai wannan Audio na Barka Da Sallah Na Zamani zai faranta maka rai, haka ke ma idan kina yin soyayya, za ki ji daɗin shi, kar ku sake a ba ku labari.


Bidiyo na saurare kawai

Audio ne wanda Sanusi Kabir ya shirya, ya kuma tsara, sannan ya gabatar da shi da kansa, don jin daɗin masoya.


Lallai kada ku bari a ba ku labari.

Idan kana da matsala a Soyayya musamman wajen rubuta Saƙonnin Soyayya ko furta lafazin soyayya, don yabon kwalliyar masoyiyarka, ko don aika mata da saƙon barka da sallah, ba shakka wannan zai nishaɗantar da kai ya kuma ƙara inganta tasirin soyayyar ta a farfajiyar zuciyarka. 


Ya kuma taimaka maka wajen tura wa masoyiyar ka saƙonnin soyayya na zamani.


DUBA WANNAN: Sauke Zazzafan Sakon Barka Da Shan Ruwa Audio Na Sanusi Kabir 


Idan har kana sauraro to ba za ka san lokacin da shauƙin soyayya zai ziyarci farfajiyar zuciyarka ba. Abin dai ba a magana.


Wato tsayawa bayyana abin da wannan maƙala ta sauti ta ƙunsa kamar ɓata lokaci ne, abin sai wanda ya saurara.


Kar dai mu cika ku da surutu ku hanzarta sauke Audio na Barka Da Shan Ruwa yanzu a kyauta, domin sauraro cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

SAUKE ANAN


KADA KU SAKE A BA KU LABARI

Da fatan zai nishaɗantar, ya kuma zama silar ƙarfafa alaƙa a tsakanin masoya.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya na saurare da na karantawa.

Friday 19 April 2024

Hukunce-Hukunce 8 Na Rancen Airtime Na Layi

Hukunce-Hukunce 8 Na Rancen Airtime Na Layi

A Azumin bara (1436H) an mini tambaya game da bashin da kamfanin MTN yake ba wa masu mu’amala da shi. Ka ranci airtime na misalin N50, a ba ka na N45. A karon farko na bayar da amasar cewa, Haramun ne! Kuma zai shi ga babin ribal Qardh!.

Hukuncin Rancen Airtime Na Layi
Hoto: Tingtel



Daga baya na janye wannan fatawar saboda yadda na ƙara fahimtar mas’alar, na ba da fatawar halaccin ta, saboda dalilai kamar haka:

1. Wannan mas’ala ba bashi ne na kuɗi da kuɗi ba, ballantana batun ribal Kardh ta zo.

2. Abin da yake haƙiƙanin mas’alar shi ne, wani ne mai amfani ne da wannan kamfani na MTN ya sayi hidima ta aritime (airtime service) wadda suke sayar da ita N45, sai suka sayar masa ita a N50.

3. Kasancewar an ambaci kuɗi a ciki ba shi yake tabbatar da cewa kuɗi da kuɗi ne aka yi musanyan su ba. An yi musanyan kuɗi ne da wata hidima (airtime service) wanda masu ita suka ƙi ba shi ita a farashin da suke sayar da ita kuɗi hannu, suka ƙara masa wani abu akai. Wannan ba komai ne ba a shari’ance ba, saboda kayansu ne, suna da damar su yi maka ƙari kamar yadda suke da damar su yi maka ragi, kuma ka karɓa.

4. Abin da zai tabbatar maka da cewa, wannan abin da ka nema su ba ka ba tsurar kuɗi ne ba, hidima ce kawai, wanda aka ba shi ita a wayarsa ba za iya sayen komai da wannan ba a gurin wani ya ce yana da kuɗin biya a gurinsa, a she ka ga ba kuɗi ne ba, koda an rubuta alamar kuɗi a tare da shi.

5. Kamar yadda ya halatta katin waya na N100 a sayar wa da mai buƙata akan N110, duk da cewa ga shi a rubuce an rubuta N100. Ko a sayar masa da shi N95, wanda babu wani masani da ya taɓa cewa, wannan riba ce ko haramun ne, saboda musanyar kuɗi da kuɗi ne. Domin alal haƙiƙa wannan katin wayar mai ɗauke da N100 a kansa ba kuɗi ne ba, wata hidima ce, aka yi mata ramzi da wannan 100, shi ya sanya da zarar ka kankare ka shigar da ita cikin wayarka  za ka jefar da wannan katin tare da cewa an rubuta kuɗi a jiki, To wannn masa’al ta rance kamar haka take, don haka, duk wanda ya haramta wannan to wajibi ya haramta sana’ar sai da kati. Wanda ba na  jin akwai mai faɗar hakan.

6. Don haka ba magana ce ta an ba ni fatawa a baibai ba, magana ce ta sake nazari akan fatawar farko, wanda wannan abu ne sananne a gurin manyan malamanmu magabata da suke canza fatawoyinsu yayin da wasu dalilai suka bayyana gare su.

7. Wannan matsaya kuma shi ne matsayar wasu daga cikin abokai na ɗaliban ilimi bayan sun kalli mas’alar ta mahanga lilimi da sanin abin da ake kira riba, daga cikinsu akwai abokina Dr. Bashir Aliyu Umar kamar yadda daga baya na samu labari. 

8. Daga ƙarshe ina kira ga sauran ‘yan uwana ɗiliban ilimi mu yi kaffa-kaffa wajen sakin baki game da sha’anin halal da haram, al’amarin yana da haɗari. sanin madafar shari’a ta wanda ya karanta ta ne.

Allah ya sa mu dace. Amin. 

Wednesday 10 April 2024

Karanta Sababbin Hadaddun Kalaman Barka Da Sallah Na Musamman

Karanta Sababbin Hadaddun Kalaman Barka Da Sallah Na Musamman

BUGUN ZUCIYA


Tamkar yadda duk taurari su zamo 'yan rakiyar zahra, to haka duk matan duniya su kasance 'yan rakiya a gare ki. A wannan ranar farin ciki, zan so a ce farin cikin ki ya zarce na kowa, tamkar yadda kwalliyar ki ta fi ta kowa, haka ma nake son murmushin ki ya zarce na kowa. Fatima ba zan iya cewa ga irin kyawun da za ki yi ba a yau, amma tabbas zan iya cewa, babu wani ido wanda zai kalle ki sau ɗaya, bai ji yana son sake kallon ki a karo na biyu ba, domin kwalliyar ki ta fi a bar ki ki yi tafiya a kan ƙasa Fatima. Ina yi miki Barka Da Sallah Fatima Mami bugun zuciyata, kuma farin cikina, daga naki Real Ababiyo. Ni Real Ababiyo nake cewa da ke, na gode tare da Barka Da Sallah!


Barka Da Sallah
Hoto: Dreams Time


MURMUSHI


Ki kan saka ni murmushi, koda kuwa a sanadin ki ne nake fushi, kin san dalili? Ba zan iya kallon kyakkyawar fuskar ki a lokacin da na shiga damuwa ba, face sai wannan damuwar ta wanke daga zuciyata. Ubangiji bai saukar da cuta ba, sai da ya saukar da maganin ta. Don haka, har kullum ina farin ciki da cewa, na same ki a matsayin maganin cututtukana. Dukkan wata cuta da ke damuna, ke ce maganin ta, ba lallai ki sani ba, amma ni dai na sani ke ce maganina. Barka Da Sallah. Ina son ki, ina ƙaunar ki. Ina Son Ki!


KWALLIYA


Idan zan bai wa kowacce mace maki da na gani bisa kwalliyar ta, to kuwa bisa adalci, ban ga wacce ta kai na ba ta ɗaya bisa ɗarin maki ba, amma duk da cewa ban ga taki kwalliyar ba, ina mai sanar da ke a matsayin wacce ta lashe gasar kwalliyar wannan ranar, kin ci ɗari bisa ɗarin maki. Ina son ki!


TSORO


Masoyiyata kin san ne mene ne? Sabo da kallon ki da na yi, duk wacce na gani a taron idin nan, sai na riƙa ji tamkar turo ta aka yi ta ba ni tsoro, ban ƙara gasgata kyawun da kike da shi ba, har sai da na tsinci kaina a tsakiyar waɗanda ba sa da kyan. Da fatan kin yi sallah lafiya? 


KISHIYA


Tamkar yadda jan fure ba zai yi wuyar gane wa a cikin koren ciyayi ba, to haka ma ko a cikin mata miliyan kika kasance, ba za ki yi wuyar ganewa ga wanda ya kalla ba. A gurin kyawu kam, ban taɓa ganin kishiyar ki ba. Fatana dai kin yi sallah lafiya?


MATSALA


Na tafiyar da kowacce daƙika ta daren jiya cikin tunanin ki, ban iya yin tunanin komai ba, har gari ya waye, bayan na tafi sallar idin, na yi mamaki, ganin cewa duk macen da na kalla, fuskar ki nake gani a cikin ta ta, hakan kaɗai ya sa na gane cewa, idan ban gan ki  a yau ba, to akwai matsala. Barka Da Sallah.


MUTUWA


Farin cikin ki ne, farin cikina. A kodayaushe ina son kasancewa a gefen ki, ina son zama kusa da ke, ba na son na yi nesa da ke idan ba dole ba.  A gaskiya ina son ki. Ke ce rayuwata dukkan ta, abokiyar zuciyata, ina matuƙar son ki, ke komai ce a gare ni, ba zan rabu da ke ba, idan ba mutuwa ba ce ta ɗauki raina ba. Ina son ki 'yammata. Barka Da Sallah. Ina son ki!


KEWA


Wannan saƙona ne na Barka Da Sallah zuwa gare ki Maryam Malesh. Yau rana ce ta farin ciki, amma lokaci mafi farin ciki a gare ni, shi ne lokacin da na samu kaina a gaban ki, anan ne zan ba wa idanuwana abin da su daɗe su na son gani. Zan ba wa kunnuwana sautin da su daɗe su na son ji, sannan zuciyata za ta samu farin cikin da ta daɗe ba ta samu kamar sa ba, a duk lokacin da na tsaya a gaban ki, zan so ki dubi cikin idanuwana, za ki ga yadda su yi kewar ki, sannan za ki ji yadda zuciyata take buga wa a domin ki, Maryam Malesh ba ni da irin ki a raina, ba ki da tamka a raina, haka kuma ba ni da kamar ki. Ni nake yi wa Maryam Malesh Barka Da Sallah, fatan kin yi sallah lafiya? Daga naki Real Ababiyo, na gode da saurarena.


Ba zan iya tuna halin da na kasance ba kafin haɗuwar mu, amma tabbas zan iya faɗar halin da zan iya tsintar kaina a ciki, idan har nan gaba rabuwa ta shiga tsakanin mu, ba lallai ba ne ki fahimci damuwata ko abin da nake nufi ba, amma dai ina gujewa kaina rasa ki, rasa ki a gare ni babbar jarabawa ce,  wacce ba lallai ba ne na iya cinye ta ba, ba na fatan Allah ya jarabce ni ta hanyar raba ni da ke ba. Ina son ki, ina burin kasancewa tare da ke, har iya ƙarshen rayuwata, ba na son na yi nesa da ke idan ba dole ba. Barka da sallah. Ina son ki.


MURNAR SALLAH


Aminci a gare ki Hafsat, na turo miki wannan saƙon ne domin taya ki murnar wannan rana wato sallah. A wannan rana na san farin cikin kowa, wunin ne, yayin da ni kuma farin cikina ke ce ba wunin ba, domin na san duk tsayin wunin ba zai wuce sa'o'i goma sha biyu ba, ya wuce, yayin da ke kuma za ki kasance a cikin zuciyata na tsawon lokacin da zan kasance a raye. Kwanaki ɗari uku da sittin na shafe ina jiran zuwan wannan ranar da zan ce miki Barka Da Sallah. Ina yi miki fatan kin yi sallah lafiya? Malama Hafsat.


RAYE


Ina son ki ne domin ban san wata macen da ta kai ki ba. Ina son ki ne domin ban taɓa ganin wata macen da ta kai ki ba. Ina son ki ne domin na gamsar da ke cewa, ke ba kamar sauran mata kike ba, kafin na haɗu da ke ban san dalilin zamo wa ta a raye cikin wannan duniyar ba, amma kuma bayan haɗuwa ta da ke, na gane cewa soyayyar ki ce dalilin da ya sa nake rayuwa a wannan duniya. Ke rayuwata ce, ke masoyiyata ce, ke komai ce a gare ni. Ina son ki, sama da yadda zan iya faɗa miki, ke ce rayuwata, sannan ina yi miki Barka Da Sallah. Ina fatan Allah ya maimaita mana bai-ɗaya. Ina son ki! 


DUHU


Da so samu ne, a ce na zamo mutum na farko da ya fara ganin ki a wannan safiya, duk da cewa ko wanka ba ki yi ba a yanzu, amma na tabbata komai kankantar hasken alfijir ya isa ya kore tarin duhun dare. Da fatan kin tashi lafiya, kuma kin wayi garin wannan rana mai albarka ta sallah. Ina son ki!


Yayinda kowa ke ɗokin shan ruwa da cin abinci, ni kuma zuciyata ta kasa yin ko ɗaya, domin a ganina ko duka ruwan duniya zan shanye ba za su iya gusar min da ƙishirwar da zuciyata take ji a sanadin soyayyar ki ba, har sai idan na gan ki ne zan iya ci ko na sha. Ina yi miki barka da safiyar sallah.


SAFIYA


Da yawa sun sa ran za su wayi garin wannan safiya, amma Ubangiji bai ba su damar hakan ba, mu da Allah ya albarkaci rayuwarmu da ganin wannan rana, mu gode masa tare da addu'ar shaida wasu ranakun sallar anan gaba. Ina yi miki barka da safiyar sallah.


AGOGO


A yau farin cikina ba ranar ba ne, face wacce nake sa ran gani a ranar, farin cikina ba na waɗanda za su kawo mana ziyara ba ne, face wacce zan kai wa ziyara da kaina. Da kowacce bugawar agogo nake ƙara ƙaguwar son ganin ki, kin tashi lafiya? Barka da wannan safiya ta sallah.


MUSAMMAN


A wannan rana ta musamman, nake miƙo gaisuwa ta musamman, ga wacce ta kasance ta musamman, a jerin mutane na musamman a rayuwata. Barka da safiyar wannan rana mai albarka. Ina son ki.


JIRA


Na tsani jira a rayuwata, amma idan ke ce wacce zan jiran, to kuwa zan iya jira na tsawon rayuwata, ba tare da gajiyawa ba, kowacce daƙika da na shafe ina jiran ki, daɗa farin ciki zai a zuciyata, hakan na nufin adadin zaman jiran ki da na yi, adadin farin cikin da zan riƙa samu a zuciyata. Jiran ki abin so ne a gare ni, ba na taɓa gajiyawa da shi, kowacce daƙika na ɓata a tare da ke, abar farin ciki ce a gare ni. Ina son ki 'Yammata. Barka da sallah, ina son ki.


MATATA


Da tafiyar kowacce daƙika ta rayuwata nake ƙara nisa a tafiyar soyayyata da ke, a yanzu Hafsat na yi nisan da wani kira ba zai taɓa sa wa na juyo ba, duk da cewa waiwaye adon tafiya ne, amma tabbas na yi imani ba zai taɓa zamo wa ado a tafiyar soyayyata da ke ba. Ina son ki Hafsat, ina matuƙar ƙaunar ki a raina, soyayyar da nake yi miki a raina Hafsat ta sanya na daina ganin mata a matsayin mata, face dai maza 'yan uwana, a cikin dukkan mata, ke kaɗai ce idona yake gani a matsayin mace. Ina son ki Hafsat, kuma ina mai tabbatar wa da duniya irin ƙaunar da nake yi miki, idan har na same ki Hafsat, zan yi farin ciki, irin farin cikin da ake cewa daɗi kashe ni. Idan na samu Hafsat a matsayin matata, to kuwa farin cikin da zan yi, har yanzu babu tunanin sa a raina. Hafsat ina gani idan na same ki, to na kammala abin da ya kawo ni duniya. A duniya dai kam, na gama dacewa, sai dai na yi kokari lahirata ta yi kyau, da auren ki zan samu rabin addinina, yayin da zan ƙara cike addinin ta hanyar kyautata miki. Ina son ki Hafsat Amira, ina ƙaunar ki Amira. Wannan saƙon daga tumaturin ki ne Hamza. Fatana dai kyakkyawata, ta yi sallah lafiya? Ina son ki, na gode da saurarena da kika yi. 


FARIN WATA


Ke kalli sararin sama, ko za ki iya faɗa min dalilin da ya sa farin wata bai fito ba a yau? To, ni na san dalili, kunyar haɗa ido yake yi da ke, ban san mai yasa ba amma na tabbata idan ya fito a yau, hasken ki ba zai bari nasa ya haska ba, kin fa yi kyau 'yammata, kyau sosai fa nake nufi. Ina son ki, kin ji. 


ZOLAYA


Da farko, da na ga wannan kwalliyar taki, bakina kasa rufewa ya yi, wallahi ban san me zan ce ba. Idan na ce kin yi kyau, na rage miki matsayi, kada ki ji kamar zolayar ki nake yi, wallahi har a raina nake faɗa miki hakan, kin yi min kyau sosai 'Yammata, ji nake tamkar na sace ki na tafi da ke, ba wannan ba ma, wai Don Allah mintina nawa ya ɗauke ki kina tsara wannan kwalliyar? Hmm 'Yammata, ko ma mintina nawa ne ƙanwata, wannan kwalliyar ba ta da tsara, na rantse.


TANTAMA


Da akwai jimloli guda uku, da ba na faɗa wa kowa su bayan ke, kuma a duk sanda na faɗa miki su, ba na nufin wasa, har a raina da gaske nake. Idan kika ji na ce ina son ki, to wallahi har a raina da gaske nake. Idan kuma ki ji na ce kin yi kyau, to har a raina hakan nake nufi, da kuma duk sanda ki ji na ce ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba, to kar ki yi tantamar hakan, kin fa yi kyau fa? Hmm  ina mai miki Barka Da Sallah.


ƘANWATA


Kin san mene ne? Sai yanzu idanuwana su samu damar karya nasu azumin, wai ta ya zan iya daina kallon ki ma? Da wannan kwalliyar dai babu wanda zai kalle ki bai ji yana son sake kallon ki ba, wallahi ƙanwata kin haɗu, haɗuwa sosai fa,  Allah dai ya tsare min ke, kar wani ya ƙwace ki daga hannuna, ke wallahi kin yi kyau sosai!


TSAWON RAYUWATA


Ana cewa, idan kana son mutum da gaske, koda za a samu dalilai dubu, da ya kamata a ce ka rabu da shi, domin su, har kullum za a samu cewa, ka nemo dalillai dubu da za a samu cewa ka ci gaba da zama da shi, na iya tsawon rayuwarka. A gurina, ban taɓa samun dalilin rabuwa da ke ba, amma a kullum sai kin ba ni wani dalilin ci gaba da son ki na iya tsawon rayuwata. Ina fatan na samu tsawon rai ne, domin na yi soyayya da ke. Ina matuƙar son ki, barka da sallah. Ina son na rayu da ke, na ci gaba da rayuwa da ke, na iya tsawon rayuwata. Ina son ki!


HUBBI


Aminci a gare ki, Habiba Hubby, da fatan wannan saƙon nawa ya same ki cikin daddaɗan yanayin da za ki iya fahimtar siyaƙin sa. Na turo miki wannan ne domin na taya ki murnar wannan rana mai albarka wato sallah.  A wannan rana na san farin cikin kowa, wunin ne, yayin da ni kuma farin cikina saɓanin yadda suke tunani ne, ke ce farin cikina, ba wunin ba, domin na san duk tsayin wunin ba zai wuce sa'o'i goma sha biyu ya wuce. Yayin da ke kuma za ki ci gaba da kasancewa a cikin zuciyata na tsawon lokacin da zan kasance a raye. Habiba Hubby, na tsawon waɗannan kwanaki talatin da mu shafe muna azumi, babu abin da zuciyata ta kasance tana yi face tunanin ki, babu abin da idanuwana su kasance su na son gani face fuskar ki, haka ma babu sautin da kunnuwana su daɗe su na mararin ji sama da sautin muryar ki. Ina so a yau, na yi tozali da kyakkyawar halittar da Allah bai taɓa nuna min kalar ta ba. Ina so a yau na ga kyakkyawar sarauniyar da ko a jaridu labarin kyakkyawar da ta kai ta, bai taɓa zuwa ba, ina so a yau na samu kaina a gaban kyakkyawar hubbina, ina so na samu kaina a gaban ki, ina mai furta miki ina son ki, ina mai furta miki irin yadda na yi kewar ki a raina, wallahi Hubbi, na yi kewar ki.


A lokacin da na fara ganin ki, babu abin da na fara tsoro sama da na faɗa miki cewa ina son ki, amma daga lokacin da na sanar da ke cewa ina son ki, babu abin da ya fi ba ni tsoro sama da rasa ki. Hubby, idan na rasa ki, na rasa rayuwata, ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba. Hubby ki fahimci irin yadda nake son ki, wallahi idan na rasa ki, zan rasa raina. Idan na rasa ki Hubby, a ina zan iya samun wacce ta kai ki? Don haka, rasa ki na nufin rasa komai a rayuwata. Idan na rasa ki, ba abin da zan tsaya tsinta a wannan duniya, dole na yi bankwana da ita, kar Allah ya nuna min wannan rana, da zan cewa duniya sai watarana.


Hubbina kin ba ni soyayyar ki, a lokacin da ya kasance cewa ba ni na fi kowa ba,  sai dai don ya kasance cewa ni kika zaɓa.


Hubbina, kin bar kowa, kin riƙe wanda ba kowa ba. Yayin da kika mai da wanda ba kowa ba, ya zama kowa a gare ki. Idan har zan iya manta wannan halarcin naki a gare ni, to kuwa har abada ba zan iya yafe wa kaina ba. Habibah zan kula da soyayyar ki, sama da yadda zan iya kula da rayuwata, haka kuma zan riƙe amanar ki, tamkar dai yadda ki riƙe tawa, ba sunana Shafi'u ba, idan har na iya bari zuciyar ki ta san wani abu koma-bayan farin ciki. Na gode da saurarena.


SAURARE


Za ki ji cewa kamar na fiye faɗa miki kalmar Ina Son Ki, ba wai ina yin hakan ba ne don sabo da na yi da furta hakan a gare ki, ina faɗa miki Ina Son Ki ne domin daɗa tunatar da ke cewa, ke ce rayuwata, matuƙar dai kika bar ni, to ni ma zan iya barin duniyar, kada ki ƙosa ko ki gajiya da saurarena yayin da nake faɗa miki cewa "Ina Son Ki". Domin ina son ki ɗin, amma ki tuna ban da kowa bayan ke, ke kaɗai nake so. Kuma ke kaɗai nake burin kasancewa tare da ke, har ƙarshen rayuwata. Ina son ki da dukkan zuciyata.


Sanusi Kabir ne ya gabatar da su, wakilin mu ya fitar da su a rubuce, ga dukkan wanda yake son ya saurare su a ainihin yadda suke, zai iya sauke Audio ɗin ta hanyar latsa nan.

Shin Ya Dace Dukkan Mata Su Fita Sallar Idi?

Shin Ya Dace Dukkan Mata Su Fita Sallar Idi?

Sunnah ce mata su fita Sallar idi kamar yadda Hadith ya kwaɗaitar da kuma maganganun magabata da suka yi bayani akan halarcin fitar mata zuwa sallar idi.


Sallar Idi
Hoto: Britannica


Marubuciya: Faridah Bintu Salis


Ummu Aɗiyyah Nusaibah Bint Ka'ab Al-ansariyyah (RA) ta ce: Annabi (ﷺ) ya yi umurni a ranar idi mata su fita, da 'ƴan mata, da mai al'ada amma ita ta nisanci wajen sallar (tunda ba yi za ta yi ba).” [Bukhari: 981, Muslim: 890]


Abdullahi Ɗan Abbas (RA) Ya ce: “Manzon ALLAH (ﷺ) Ya kasance yana umurtar ƴaƴansa. da matansa, su fita a idi guda biyu (Babba da ƙaramar Sallah).” [Sahihul Jami'i: 3888]


Sayyidina Abubakar (RA) Ya ce: “Wajibi ce Sallar Idi ga duk wacce take da kwatankwacin malulluɓi da zai rufe ta, ta fita zuwa idoji guda biyu ƙarama da Babba.” [Ibn Abi Shaibah ya ruwaito shi a Musannaf 2/182 da sanadi ingantacce] 


Alhafiz Ibn Hajar (Rahimahullah) Ya ce: “Alƙali Iyad Bn Musa ya naƙalto wajabcin Sallar idi hatta ga mata daga Abubakar da Aliyu da Ibn Umar.” [Fat-hul Baary 2/545] 


Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albaniy (Rahimahullah) Ya ce: “Toh a sani wannan shi ne gaskiya da babu ƙoƙonto a kai na wajabcin idi hatta ga mata, saboda yawan hadisan da aka ruwaito game da haka, Hadisin Ummu Aɗiyya da ya gabata ya isar mana, ba sharʼanci kawai ya ke nunawa ba, hatta wajabcin hakan yake nunawa ga su matan, saboda umarnin da Annabi (ﷺ) ya bayar, asali kama umurni wajabci ne.” [Salatul Idaini: 15] 


Sunnah ne mata su fita zuwa Sallar Idi, don haka mata ku yi ƙoƙari ku halarci Idi, sannan a kiyaye sanya turare ko bayyanar da wani abu na ado, ku lizimci hijabi na Sharia kuma ku zamto masu natsuwa da kamun kai, sannan a yayin tafiya ku kasance masu bin gefen hanya ba tsakiya ba, kuma ku kiyaye cakuɗuwa da maza, idan kuka kasance haka sai dai ace daku: MASHAA ALLAH.

Dalilin Mutuwar Jaruma Saratu Daso

Dalilin Mutuwar Jaruma Saratu Daso

Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso, ɗaya ce daga cikin manyan jaruman Kannywood, waɗanda aka daɗe ana damawa da su a masana'antar.


Marigayiya Jaruma Saratu Giɗaɗo
Hoto: Real Ali Nuhu


Ta rasu a jiya talata, bisa larurar mura da ta yi fama da ita, daga lokaci bayan lokaci.


Marigayiya Jaruma Daso
Hoto: Zaharadeen Sani Owner


Mutane da dama, sun ji mutuwar ta, kasancewar ta mace mai yawan barkwanci da jama'a, tare da taimakon marayu.


Mu na yi mata fatan samun kyakkyawar makoma.

Tuesday 9 April 2024

Karanta Zafafan Sababbin Kalaman Barka Da Shan Ruwa

Karanta Zafafan Sababbin Kalaman Barka Da Shan Ruwa

AMFANI 


Mene ne kalmar ina son ki, idan har ba zan iya yin komai a kanki ba? Mene ne ma'anar cewa ina son ki, idan har farin cikin ki ba zai iya zamo wa nawa ba? Mene ne ma amfanin soyayyar idan har ba ta zamo silar murmushin ki ba? Ba wannan ba ma, mene ne amfani na idan har ban tura miki da saƙon Barka Da Shan Ruwa Ba? Ina fatan kin sha ruwa lafiya? Ina son ki!


Barka Da Shan Ruwa
Hoto: Photo Sune


LEMA


Da zan iya yi ko zamo wa duk abin da na so a rayuwa, da kuwa zan zamo miki laima/lema, ta yadda rana ba za ta taɓa min ke ba, na zamo miki AC ta yadda ba za ki ji zafin ranar ba, na rage miki tsayin wuni, ta yadda za ki sha ruwa kafin kowa,  haka ma na ƙawata daren ki da daddaɗan iska,  ta yadda za ki yi baccin ki cikin salama. Ina son ki. Barka Da Shan Ruwa! Fatan kin sha ruwa lafiya?


ZAFI


Da a ce kina kusa da ni, na sani wuni ba zai yi min tsawo ba, duniyar ba za ta yi min zafi ba, haka ma maƙogwarona ba zai bushe ba, da a ce kina a tare da ni, na sani ƙarfina ba zai ƙare ba, wahala ba za ta kusance ni ba, haka ma  cikina ba zai yunwa ba, kuma da a ce kina kusa da ni, na sani ba zan yi wahalar rubuto miki saƙon Barka Da Shan Ruwa Ba!  Zan faɗa miki ne kai-tsaye, fatan kin sha ruwa lafiya? Ina son ki! 


SAƘO 


Idan har farin cikina zai iya zamo wa naki, damuwarki kuma tawa, to kuwa ki saka a ranki, duk sanda azumi ya ba ki wahala, ya ba ni kwatankwacin ta. Duk sanda azumi ya ba ki wahala, zan iya ganewa, domin kuwa ni ma zan ji a jikina. Ina fatan sakona ya same ki cikin koshin lafiya, kuma ina miki fatan an sha ruwa lafiya. Barka Da Shan Ruwa.


BUƊA BAKI 


Zan so zamo wa ruwan sanyin da kike sha, yayin buɗa baki, domin na sanyaya zuciyar ki, kuma zan yi burin rikiɗewa zuwa ruwan ɗumin da kike fara saka wa cikin ki, domin samar miki da natsuwa a yayin buɗa baki. Ina ma a ce zan iya zamo wa hatta abincin da kike taunawa da ƙayatattun haƙoran ki, da kuwa farin ciki ba a magana, har abada fatana ba ya wuce zamo wa gaba-daya naki. Ina Son Ki. Barka Da Shan Ruwa.


GORO


Na kasa yarda da karin maganar Hausawa da suke cewa, "Rai dangin goro, sai da hutawa.". Domin kuwa tun da na fara son ki nake ji a raina, hutu ba nawa ba ne. Idan hannuwana ba sa aikin rubuta saƙo a gare ki. To, kuwa su na nan riƙe da waya ina magana da ke. Da baki ya ƙare nasa aikin, ido yake fara   aikin kallon hoton ki. Aikin zuciya kam, a kullum tunanin ki ne, har zuwa sanda bacci zai ɗauke ƙwaƙwalwata zuwa duniyar mafarkin ki, a dai irin waɗannan ayyukan, mutuwa ce kaɗai za ta sa na huta. Ina Son Ki. Barka Da Shan Ruwa.



HAUKA


Su na cewa "So dangin hauka.". Amma ni saɓanin haka na gani, bayan faɗawa ta ki soyayyar, a da ba ni da aikin yi, amma a yau na samu aikin tunanin ki, a da ban damu da kowa ba, a yau kuma Allah ya ban wacce nake matuƙar damuwa da ita, da ba ta kulawa. A da ban da wata manufa, amma a yau kin fuskantar da tunanina zuwa ga raya sunnar babban masoyina Annabi Muhammad (S.A.W), ai kuwa kin ceto rayuwata, kin ba wa rayuwata manufa. Ina son ki. Barka Da Shan Ruwa.



ALKAWARI


Idan kika ɓuya, zan gano ki. Idan ba kya nan zan nemo ki. Idan kuma kika tafi, zan jira ki, amma fa idan wani ya yi kuskuren raba ni da ke, to kuwa dole zan yaƙe sa, domin ke tawa ce ni kaɗai, ba zan taɓa iya raba soyayyar ki da kowa ba a duniya. Da a ce 'Yan Adam su na da iko akan komai, da kuwa na ba ki damar shiga zuciyata don ki ga hakikanin girman son da nake yi miki a zuciyata, amma tunda ba zan iya hakan ba, alƙawari ne a kaina zan ci gaba da sanar da ke yadda nake son ki a zuciya, har zuwa ranar da zuciyar ki za ta gamsu cewa soyayyata a gare ki gaskiya ce.


NI'IMA


Da a ce ni kurma ne, zan iya jin ki ne ta hanyar murmushin ki, da kuwa ni bebe ne, zan iya magana da ke ta idanuwan ki, da na kasance makaho kuma da kowacce bugawar zuciyar ki, zan san ma'anar ta. Wasu lokutan, idan na ƙura miki ido, sai na riƙa mamakin yadda wani kafin ni bai taɓa ganin abin da ni nake iya gani a tattare da ke ba, ina kasa fahimtar yadda wani bai taɓa ganin tsantsar kyawun da Allah ya ajiye a tattare da ke ba, amma kuma na kan gode wa Allah da ya sa ba wanda ya taɓa lura da hakikanin baiwar da Allah ya ajiye a tattare da ke, domin kuwa da hakan ya faru, da zuwa yanzu wasu ne akan matsayin da nake a yanzu. Na gode wa Allah da ya ni'imta ni da babbar ni'ima a rayuwata.


Sanusi Kabir ne ya gabatar da su, wakilin mu ya fitar da su a rubuce, ga wanda yake son ya saurare su a ainihin yadda suke, zai iya sauke Audio ɗin ta hanyar latsa nan.
KARANTA YADDA AKE YIN KABBARORI DA KARAMAR SALLAH

KARANTA YADDA AKE YIN KABBARORI DA KARAMAR SALLAH

Yin kabbarori Sunnah ne mai ƙarfi a sallar Idi ƙarama(Idul fitr). saboda fadin Allah:

"وَلِتُكْمِلُوا الْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا اللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَاكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ".


YIN KABBARORI DA KARAMAR SALLAH
Hoto: Holiday Times


"...kuma dõmin ku cika adadin, kuma dõmin ku girmama Allah a kan Yã shiryar da ku, kuma tsammãninku, zã ku gõde".


Lokacin farawa daga ganin watan Shawwal, ma'ana daga faɗuwan ranan ƙarshe na watan Ramadhan.


Ibnu Abbas ya ce: "Haƙƙi ne a kan dukkan musulmi idan sun ga watan Shawwal su yi Kabbara".  Lokacin yana ƙarewa ne daga fitowan liman zuwa gabatar da  sallah".


Sigan Kabbarorin:


ALLAH AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLALLAH, ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD.


Tushe/Asali: Zauran Daliban Ilimi

Sauke Zazzafan Sakon Barka Da Shan Ruwa Audio Na Sanusi Kabir

Sauke Zazzafan Sakon Barka Da Shan Ruwa Audio Na Sanusi Kabir

 Wannan Audio na "Barka Da Shan Ruwa" cike yake da zafafan sakonnin soyayya masu ratsa sassan zukatan masoya. Idan har kana sauraro to ba za ka san lokacin da shauƙin soyayya zai ziyarci farfajiyar zuciyarka ba. Abin dai ba a magana.


Saƙon Barka Da Shan Ruwa
Hoto: Wallpaper Cave

Idan har kana soyayya, lallai wannan Audio na Barka Da Shan Ruwa zai faranta maka rai, haka ke ma idan kina yin soyayya, za ki ji daɗin shi, kar ku sake a ba ku labari.


Bidiyo na saurare kawai


Audio ne wanda Sanusi Kabir ya shirya, ya kuma tsara, sannan ya gabatar da shi da kansa, don jin daɗin masoya.


Lallai kada ku bari a ba ku labari.

Idan kana da matsala a Soyayya musamman wajen rubuta Saƙonnin Soyayya ko furta lafazin soyayya, don yabon kwalliyar masoyiyarka, ko don aika mata da sakon barka da shan ruwa, ba shakka wannan zai nishaɗantar da kai ya kuma ƙara inganta tasirin soyayyar ta a farfajiyar zuciyarka. Ya kuma taimaka maka wajen tura wa masoyiyar ka saƙonnin soyayya na zamani.


DUBA WANNAN: Sauke Zazzafan Sakon Murnar Sallah Audio Na Sanusi Kabir A Kyauta


Wato tsayawa bayyana abin da wannan maƙala ta sauti ta ƙunsa kamar ɓata lokaci ne, abin sai wanda ya saurara.

Kar dai mu cika ku da surutu ku hanzarta sauke Audio na Barka Da Shan Ruwa yanzu a kyauta, domin sauraro cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

SAUKE ANAN


KADA KU SAKE A BA KU LABARI

Da fatan zai ilimantar,nishaɗantar ya kuma faɗakar da masoya gaba-ɗaya. Ya kuma zama silar ƙarfafa alaƙa a tsakaninsu.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya na saurare da na karantawa.

Friday 5 April 2024

 Kalli Hotunan Nura M Inuwa A Fagen Aiki

Kalli Hotunan Nura M Inuwa A Fagen Aiki

Nura Musa Inuwa, wanda aka fi sani da Nura M. Inuwa, ba ɓoyayye ba ne a masana'antar Kannywood, domin kusan babu wanda yake sauraren wakokin soyayya a baya, ko a yau wanda bai san shi ba.


Nura M. Inuwa
Hoto: Nura M. Inuwa


Hotunan sun ɗauki hankula sosai a shafukan Sada Zumunta duba da yanayin yadda aka ɗauki hotunan, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin duniya.


Mawaƙi Nura M. Inuwa
Hoto: Nura M. Inuwa


An ɗauki kyawawan hotunan ne a lokacin da yake fagen aiki, a cikin situdiyo (Studio).


Nura M. Inuwa
Hoto: Nura M. Inuwa


Waɗannan wasu ne daga cikin kyawawan hotunan sa.


Ƙalli ƙarin wasu hotunan a ƙasa;


Mawaƙi Nura M. Inuwa
Hoto: Nura M. Inuwa

Nura M. Inuwa
Hoto: Nura M. Inuwa

Mawaƙi Nura M. Inuwa
Hoto: Nura M. Inuwa


Fatan hotunan nasa, sun burge masoyan sa.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun sababbin hotunan mawaƙan ku, masu inganci.

Tuesday 2 April 2024

Kalli Zafafan Hotuna Daga Dandalin Daukar Shirin Gidan Sarauta Zango Na Biyu

Kalli Zafafan Hotuna Daga Dandalin Daukar Shirin Gidan Sarauta Zango Na Biyu

Gidan Sarauta, ɗaya ne daga cikin sababbin shirye-shirye masu dogon zango na masana'antar Kannywood, wanda aka kammala ɗaukar zango na biyun shi a halin yanzu.


Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy


Gidan Sarauta, ya samu karɓuwa yadda ya kamata, a kusan ko'ina.


Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

A yanzu haka, an kammala haska zangon farko na  shirin, har sai zuwa ga ranar 13-4-2024 za a dawo daga hutun da aka tafi, na kammala zangon farkon, domin ci gaba da haska zango na biyun, wanda ya kasance ci gaban na farkon ne.


Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Waɗannan wasu ne daga cikin hotunan dandalin ɗaukar shirin Gidan Sarautar.


Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy


Ƙalli ƙarin wasu hotunan a ƙasa:



Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Dandalin Ɗaukar Shirin Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Yayin Ɗaukar Shirin Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Fatan hotunan, sun burge ku.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun hotuna da labaran abubuwan da ke faruwa a dandalin ɗaukar shirye-shiryen wasan kwaikwayo, masu gajeren zango, har ma da na shirye-shirye masu dogon zango.